An kafa dokar ta ɓace a Pakistan | Labarai | DW | 04.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar ta ɓace a Pakistan

Hukumomin ƙasar Pakistan, sun capke a ƙalla mutane 500 ,a sakamakon dokar ta ɓacen da shugaba Pervez Musharaf ya girka jiya.

Shugaban ya kafa wannan doka, tare da rushe kunɗin tsarin mulkin ƙasa, da kuma tsige shugaban kotun ƙoli, wanda ya bayyana haramcin dokar.

Musharaf ya ɗauki wannan mataki,a yayin da ya rage wattani 2, a gudanar da zaɓen yan Majalisun dokoki.

Sakataran harakokin wajen na Ƙungiyar Tarayya Turai Havier Solana, yayi kira ga hukumomin Islamabad, su shirya zaɓen yan Majalisun Dokoki, kamar yadda a ka tsara da farko, wato watan Janairu na shekara mai zuwa.

A cewar EU, girka dokar ta ɓace ba zai kawo ƙarshen ta´adanci ba.

A halin da ake ciki, jami´an tsaro sun ja ɗamara a sassa dabam-dabam na ƙasar, da zumar murƙushe duk wata zanga-zanga.

A gobe ƙungiyar alƙalai ta ƙasa ta shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da wannan doka.