An kafa dokar hana fita a Chadi | Labarai | DW | 01.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokar hana fita a Chadi

Hukumomi a Chadi sun sanar da sanya dokar kulle a N'djamena babban birnin kasar, a karo na farko tun bayan bullar annobar corona.

A wata dokar da Shugaba Idriss Deby na kasar ya sanya wa hannu a yau Juma'a, gwamnatin ta ce babu fita daga ketowar alfijir har i zuwa faduwar rana a wannan birni, saboda yadda ake ganin cutar corona ke yaduwa cikin hanzari.

Kafin yanzun dai Chadin ba ta da wadanda cutar ta kama sosai, idan aka danganta da kasashen da kewaye da ita, inda tun cikin watan Maris na bara take da mutum 2,113 da suka kamu yayin da ta kashe wasu 104.

To sai dai kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ce a baya-bayan nan ana samun ninki cikin kalilan na adadin wadanda suka kamuwa da cutar a N'djamena, inda ko a yau din nan akwai mutum 36 da suka kamu.

Dokar dai ta tsawon mako guda ce a birnin na N'Djamena.