An kaddamar da hare-hare kan IS a Siriya | Labarai | DW | 23.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kaddamar da hare-hare kan IS a Siriya

Dakarun Amirka da na wasu kasashen Larabawa sun kaddamar da hare-hare kan 'yan kungiyar nan ta IS har ma hakan ya yi sanadiyyar hallaka mayakan IS din sama da 20.

Symbolbild Algerien Geiselnahme Islamischer Staat Franzose

An kai galibin hare-haren ne kan IS ta hanyar amfani da jiragen yaki

Baya ga wadandan aka hallaka, masu aiko da rahotanni sun ce da dama daga cikin 'yan kungiyar sun jikkata wasunsu ma munana a fatatawar da aka yi da su birnin nan na Raqqa da yankunan da ke kewaye da shi.

Gabannin fitar wannan labarin dai, hukumar tsaron Amirka ta Pentagon ta ce dakarun kasar da na kawayenta sun fara afkawa mayakan na IS wanda suka kame wasu yankuna a kasar Siriya da Iraki har ma suka ayyana kafa daular Musulunci.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu