An kaddamar da gagarumin shirin inganta rayuwar ´yan asalin kasa a Kanada | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kaddamar da gagarumin shirin inganta rayuwar ´yan asalin kasa a Kanada

Gwamnatin kasar Kanada da shugabannin ´yan asalin kasar sun albarkaci wani gagarumin shiri na biliyoyin Euro da nufin yaki da matsalar talauci da ta yiwa al´umar ´yan asalin kasar katutu. FM Paul Martin da Firimiyoyin larduna 13 na kasar suka ba da sanarwar wannan gagarumin aiki na tarihi bayan wani taron koli na kwanaki biyu da suka gudanar da kungiyoyin ´yan asalin kasar. Za´a yi amfani da kudaden akan wasu shirye-shirye na tsawon shekaru 10 da nufin inganta muhalli, kiwon lafiya, samar da ilimi mai nagarta da kuma kyautata halin rayuwar ´yan asalin kasar. An gabatar da wannan shiri ne a daidai lokacin da jam´iyun adawa ke shirin daukar matakan kifar da gwamnatin FM Martin maras rinjaye a ranar litinin kana kuma su tilasta shirya sabon zabe a cikin watan janeru.