An kaddamar da allurar rigakafin shan Inna a Lebanon | Labarai | DW | 04.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kaddamar da allurar rigakafin shan Inna a Lebanon

Hukumar taimakon yara ta Mdd, wato Unicef tace ta fara yiwa dubbannin yaran kasar Lebanon allurar rigakafin cututtukan shan Inna da kyanda da kuma cututtuka dake da dangantaka da wadan nan.

Shirin wanda aka kaddamar dashi da tallafin hukumar lafiya ta kasar, an shaidar da cewa anyi hakan ne da nufin yin rigakafin bullar wadan nan cututtuka, a sakamakon rashin gidajen kwana ga daruruwan iyaye bisa rikicin Israela da Hizbullah.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, karkashin shirin an yi hasashen yiwa yara dubu dari takwas allurar rigakafin, wadanda da yawa yawan su na zaune a matsugunai marasa tsafta, a sakamakon rushe musu gidaje da Israela tayi ta hanyar kai hare hare.