An kada kuri′ar zaman iyalan baki a Jamus | Labarai | DW | 01.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kada kuri'ar zaman iyalan baki a Jamus

Majalisar wakilan Jamus ta kada kuri’a kan sake maido da dokar da za ta ba da dama ga ‘yan gudun hijira su kawo iyalansu zuwa kasar.

Bundestag Abstimmung Familiennachzug Merkel (picture-alliance/AP/M. Sohn)

Batun 'yan gudun hijira na da muhimmanci a siyasar Jamus

Daga ranar daya ga watan Agusta iyalan  bakin hauren 1,000 ne za a rika basu damar zuwa Jamus a duk wata, muddin dai suna da alaka ta kai tsaye da ‘yan gudun hijirar da ke zaune a kasar ta Jamus.

Wannan sabuwar dokar da jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Angela Merkel CDU da jam'iyyar SPD suka gabatar, ‘yan majalisa 376 ne suka amince da ita yayin da 248 suka ki aminta. A cewar ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere wannan mataki ne me muhimmanci.

A watan Maris na shekarar 2016 ne dai gwamnatin ta Jamus ta tsayar da ba da dama ga ‘yan gudun hijira da ke da kwarya-kwaryar izinin zama su hade da iyalansu. Jamus dai ta yi marhabun ga 'yan gudun hijira 890,000 a shekarar 2015.