1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta batun fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai

Suleiman Babayo
December 17, 2018

An jinkirta muhawara da kada kuri'a a majalisar dokokin Birtaniya kan ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai zuwa watan gobe na sabuwar shekara.

https://p.dw.com/p/3AH94
Großbritannien Theresa May, Premierministerin | im House of Commons
Hoto: picture-alliance/empics/House of Commons

Majalisar dokokin Birtaniya za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar fita daga kungiyar Tarayyar Turai a tsakiyar watan gobe na Janairu na sabuwar shekara ta 2019. Firaminista Theresa May ta ayyana haka a wannan Litinin yayin muhawara a majalisar dokokin, wanda aka dakatar domin ci gaba da yi ranar 7 ga watan gobe na Janairu.

Idan majalisar ta koma muhawara 7 ga watan na Janairu sabuwar shekara ta 2019, mako guda daga bisani za a kada kuri'a kan batun na ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai. Lokacin tattaunawar jagoran 'yan adawa Jeremy Corbyn na jam'iyyar Labour ya caccaki Firaminista Theresa May saboda jinkirta kada kuri'ar a majalsiar dokokin ta Birtaniya. Akwai 'yan majalisa da dama na bangaren jam'iyya mai mulki ta Conservative gami da jam'iyyar adawa ta Labour da suka harzika kan matsayin gwamnatin Birtaniya a kan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai da yadda firaminitar take jan kafa.