An janye yaji aikin ma′aikata a jihar Filaton Najeriya | Labarai | DW | 20.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An janye yaji aikin ma'aikata a jihar Filaton Najeriya

Bayan watanni bakwai suna yajin aikin neman biyansu ƙarin albashi, ma'aikata a Filato sun janye yajin aikin bayan yarejeniyar da suka cimma da gwamnati.

Ƙungiyar ƙwadago a jihar Filato a arewacin Najeriya ta sanar da janye yajin aikin da take na tsawon watanni bakwai, sakamakon tsoma bakin da gwammatin tarayya ta yi. Da yammacin wannan Alhamis ne 'yan kwadagon suka sanar da janye yajin aikin jim kaɗan bayan wata ganawa tsakanin wakilan kwadago na ƙasa, da na gwamnatin Filato, tare da ministan kwadago na Najeriya a Abuja. Cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin mu na Jos, Abdullahi Maidawa Kurgwi, shugaban kungiyar kwadago a jihar Filato Jibrin Bancir, ya ce gwamnatin jiha ta amince za ta biya sabon albashi na Naira dubu 18, tare kuma da biyan kudin watanni uku kai tsaye ba tare da wani ɓata lokaci ba. Gwamnatin ta Filato ta amince da cewar za su zauna tare da wakilan 'yan kwadago na kasa da wakilin gwamnatin tarayya, domin su tsara yadda za'a biya sauran albashin baya na ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar, somawa daga watan Yuni zuwa Satumba na wannan shekara. Tare da wannan matsayar, yanzu shugabannin kwadagon sun janye yajin aikin ma'aikata a jihar Filato daga wannan Alhamis.

Mawallafa: Abdullahi Maidawa Kurgwi / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman