An ja kunnen masu zanga-zanga a Tunisiya | Labarai | DW | 11.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ja kunnen masu zanga-zanga a Tunisiya

Hukumomi a Tunisiya sun bukaci masu zanga-zanga kan su dakartar da boren da suke yi daidai lokacin ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce ta cafke mutane kimanin 200 da ake zarginsu da hannu a tashin hankali da ake fuskanta.

Boren da Tunisiya ke fuskanta a halin yanzu dai na da nasaba da matakan tsuke bakin aljihu da aka dauka wanda suka haifar da hauhawar farashin kayyayaki, lamarin da 'yan kasar ke cewar ya jefasu cikin wani hali. Baya ga kame da aka ce an yi, rahotanni na cewar an jikkata 'yan sanda akalla 50.

Hukumomi a kasar sun ce za su dau mataki na ladabtarwa kan masu shirya boren da kasar ke fuskanta bayan da aka jiyo wasunsu na cewar za su gudanar da gagarumar zanga-zanga a gobe Juma'a don yin matsin lamba kan gwamnati na ta sake lalale kan matakan da ta ce ta dauka don daidaita tattalin arzikin kasar.