An harbe mataimakin Firaministan Iraki Abdel Mahdi har lahira | Labarai | DW | 30.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An harbe mataimakin Firaministan Iraki Abdel Mahdi har lahira

A Iraqi an sake kai hari akan manyan jami´an gwamnati. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar wasu ´yan bindiga sun harbe dan´uwan mataimakin FM Iraqi Adel Abdel Mahdi a birnin Bagadaza. Shi dai Abdel Mahdi shi ne mai bawa FM Ibrahim al-Jafari shawara. A wani harin kuma mukaddashin ministan cinikaiyar kasar Kais Dawud Hasan ya samu rauni a wani kwantan bauna da ´yan tawaye suka kaiwa ayarin motocinsa. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce wasu ´yan bindiga suka bude wuta kan ayarin motocin ministan inda suka kashe biyu daga cikin masu tsaron lafiyarsa.