An haramtawa Ahmed Shafiq taɓa dukiyarsa | Labarai | DW | 21.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An haramtawa Ahmed Shafiq taɓa dukiyarsa

Ma'aikatar harkokin shari'ar Masar ta bada sanarwar sanya doka kan taɓa kuɗi ko kuma kadarorin da tsohon firaministan Masar Ahmed Shafiq ya mallaka a ƙasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar shari'ar ta Masar Ahmed Roshdy Sallam ya ce ma'aikatar ta ɗau wannan mataki ne domin gudanar da bincike kan dukiyar ta Ahmed Shafiq, wanda yanzu ake shirin gurfanar da shi gaban kotu kan zargin da ake yi masa na halasta kuɗaɗen haram lokacin da ya ke kan gadon mulki.

Sanarwar har wa yau ta haramtawa 'ya'yan Shafiq ɗin mata su uku su taɓa wata kadarar da su ka mallaka a ƙasar ko kuma tsabar kuɗi har sai an kammala bincike.

A ranar biyu ga watan Disamba mai zuwa ne dai ake sa ran fara shari'ar ta Ahmed Shafiq wanda yanzu haka ke zaune a haɗaɗɗiyar daular laraba tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a wata Yunin da ya gabata.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu