1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An haramtawa Blatter da Platini harkar kwallon kafa

Yusuf BalaDecember 21, 2015

Wannan hukunci na tsawon shekaru takwas na haramta musu shiga harkar kwallon kafa,dai ya kawo karshen shekaru da Mista Blatter ya yi a wannan fage na kwallon kafa yana jan raganar hukumar ta FIFA.

https://p.dw.com/p/1HR8j
Schweiz FIFA PK Blatter
Blatter da yake jawabi bayan dakatar da shiHoto: Getty Images/P. Schmidli

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Joseph Blatter da shugaban hukumar kwallon kafa ta Tarayyar Turai UEFA Michel Platini daga ranar Litinin din nan an haramta musu shiga duk wata harka da a shafi kwallon kafa tsawon shekaru takwas nan gaba kamar yadda kwamitin da a na hukumar da ya binciki tabar gazar cin hanci a hukumar ya bayyana.Wannan hukunci dai ya kawo karshen shekaru da Mista Blatter ya yi a wannan fage na kwallon kafa yana jan raganar hukumar ta FIFA, sannan ya kuma rushe mafarkin da Platini ke yi na shugabantar wannan hukuma a nan gaba.Kwamitin ya ce ya gano cewar an karya ka'ida wajen bada kudi har Dala miliyan biyu ga Platini a shekarar 2011. Babu dai inda a rubuce ko a magance da Mista Blatter ya nuna cewa biyan kudaden ya halatta. Zargin da Mista Blatter ke cewa ba a yi masa adalci ba.

"Saboda wannan zargi na cewa na bada kyauta ba tare da na kira ta da sunan cin hanci ba zuwa ga Platini, saboda cewa a dokar FIFA zan fada da baki ko a rubuce, dan haka aka dakatar da ni tsawon shekaru takwas, to zan ci gaba da fafutika domin kaina da ma hukumar ta FIFA".