An haramta cin kasuwannin kauye a Borno | Labarai | DW | 07.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An haramta cin kasuwannin kauye a Borno

Hukumomin har ila yau sun haramta amfani da dawakai da jakuna a wani mataki na magance hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa a jihar Borno ta Najeriya.

Nigeria Selbstmordanschlag auf Markt in Maiduguri

Kasuwa a Maiduguri

Hukumomin a jihar Borno a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun sanar da haramta amfani da dawakai da jakuna a wani mataki na magance hare-haren da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa kan dawaki a sassan jihar. Haka kuma hukumomi a jihar sun haram a cin kasuwannin kauye wanda yanzu haka ake zargin ‘yan kungiyar na kaiwa hare-hare tare da kwasar kayayakin abinci da na rayuwar yau da kullum.

Rundunar Sojojin sun ce ya zama dole su dauki wannan mataki ne don kawo karshe ayyukan hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a yankin a wannan lokaci musamman ganin mayakan sun koma amfani da dawaki da jakuna watakila saboda karancin mai na ababan hawa da suke da su.