An hana yan sandan Jamus duba launin fata wajen bincike | Zamantakewa | DW | 01.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An hana yan sandan Jamus duba launin fata wajen bincike

Alkalai a nan Jamus sun tabbatar da cewar binciken takardun jama'a saboda launin fatar su ya sabawa kundin tsarin mulkin Jamus

Wani kotun daukaka kara a garin Koblenz dake nan Jamus ya yanke hukuncin da ya haramtawa yan sanda nan gaba su rika zaben mutanen da zasu yi wa bincike ta hanyar duba fatar jikinsu. Wannan hukunci ya kawo karshen takaddama ta tsawon shekaru biyu tsakanin yan sandan taraiya da wani dalibi bakar fata Bajamushe mazaunin garin Kassel.

A watan Disamba na shekara ta 2010 dalibin mai shekaru 25 dake karatun neman ilimin gine-gine kuma bakar fata dake rike da paspo na Jamus, ya kasance cikin jirgin kasa ne kan hanyarsa daga garin Kassel zuwa birnin Frankfurt. A cikin jirgin ne yan sanda suka zabe shi shi kadai domin binciken takardunsa, amma dalibin ya ga cewar wannan ba komai bane illa nuna masa wariya, saboda haka yaki nuna masu takardun nashi. Maimakon haka, yace wnanan mataki na yan sandan ya tunatar dashi irin matakan da yan Nazi suka rika dauka. Hakan ya fusatar da yan sandan wadanda suka gabatar dashi a kotu domin laifin cin mutuncinsu.

Polizei Hamburg

Binciken yan sanda kan baki

Lokacin shari'ar da aka yi ta yinta a kotuna dabam dabam, daya daga cikin yan sandan ya fito fili ya tabbatar da cewar ya zabi dalibin domin bincika shi ne saboda launin fatarsa, wanda ba wani sabon abu bane. Daga nan dalibin ya daukaka kara yana tuhumar yan sandan na taraiya da laifin nuna masa wariyar launin fata.

Wani kotu na shari'ar al'amuran mulki na yau da kullum a watan Maris na shekara ta 2012, ya yanke hukuncin cewar wannan bincike na yan sanda babu wani kuskure cikinsa, saboda a kokarin hana bakin haure shigowa Jamus, yan sandan suna iya duba siffar mutum, su bincika shi idan suna ganin dacerwar hakan. Sai dai kuma babban kotu a Koblenz ya soke wannan hukunci, ya kuma baiwa dalibin gaskiya a karar da ya daukaka. Kotun yace launin fatar mutum bai kamata ya zama abin da za'a rika amfani dashi wajen binciken takardun mutane ba. Alkalai a kotun suka ce yin haka wani mataki ne mai muni na nuna wariya, abin da aka hana karkashin fanni na ukku na kundin tsarin mulkin Jamus. Wannan fanni na kundin tsarin mulkin ya tanadi cewar babu wanda ya kamata a nuna masa wariya ko wani banbanci sakamakon jinsinsa ko addininsa ko launin fatarsa ko manufofinsa na siyasa ko kuma kasancewarsa namiji ko mace.

Wannan hukunci ya jawo muhawara tsakanin yan sanda. Shugaban kungiyar yan sanda ta kasa baki daya, Rainer Wendt yace kotuna babu abin da suka sani illa su yanke hukunci bisa shari'a kan takarda, amma babu ruwansu da yadda hakan zai shafi aiyukanmu a zahiri. Aikin yan sanda zai kara zama mai wahala a sakamakon wannan hukunci. To sai dai wata kungiyar ta yan sanda ta musunta haka. Shugabanta, Josef Scheuring ya shaidawa DW cewar irin wannan jawabi na Wendt ya kawo masa damuwa.

Feier 40 Jahre GSG9 Friedrich

Ministan cikin gida na Jamus, Hans-Peter Friedrich

"Wannan jawabi ko kadan bai zama abin da ya wakilci mafi yawan yan sandan Jamus ba, kuma babu abin da yake nunawa illa cewar kamar yan sandan Jamus suna aiyukan su ne ba bisa ka'ida ba. Babu shakka zamu amince da hukuncin kotun, kuma ko alama ba zai kawo cikas a aiyukan yan sanda ba, saboda dama can yan sandan taraiya basa gudanar da bincike sai tare da wani dalili na yin haka, ko da shike ga dalibin mazaunin Kassel babu wani dalili na yi masa bincike. Babu wanda ya kamata a zabe domin bincikensa a nan Jamus saboda dalilin launin fatarsa kadai."

Kungiyar kare hakkin yan Adam ta Amnesty International ta baiyana jin dadin ta ga wannan hukunci, inda masanin kungiyar game da aiyukan yan sanda da kare hakkin yan Adam, Alexander Bosch dake hira da DW yace kungiyarsa tana marhabin da wannan hukunci a matsayin wata alama mai karfi ta adawa da wariya.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar