An hana Laurent Gbagbo barin gidan yari | Labarai | DW | 18.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hana Laurent Gbagbo barin gidan yari

Za a ci gaba da tsare Shugaban Kasar Cote d' Ivoire Laurent Gbagbo da Charles Blé Goudé tsohon shugaban kungiyar matasa na Patriote wanda kotun kasa da kasa ta ICC ta wanke a makon da ya gabata.

Kotun ICC ta wanke Gbagbo da  Charles Blé Goudé a ranar Talata da ta gabata, amma yanzu za su ci gaba da kasancewa  a gidan kurku har zuwa daya ga watan Faibreru, bayan da alkalin alkalai na kotun ICC ya daukaka kara.Gbagbo wanda ake tsare da shi kusan shekaru bakwai a birnin Hague, an yi masa sharia'a ne kan laifuka na take hakkin dan Adama a tarzomar da ta biyo bayan zaben kasar na shekarun 2010 zuwa 2011 inda mutum sama da dubu uku suka rasa rayukansu.