1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana jami'an Birtaniya shiga Douma

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

Rasha da Siriya sun hana ba da dama ga kowa ya shiga yankin na Douma abin da ke nuna cewa Rasha da Siriya sun yi baki guda kan batun a cewar tawagar ta Birtaniya.

https://p.dw.com/p/2w7aa
London Pressekonferenz Theresa May zur Militäraktion in Syrien
Hoto: Getty Images/AFP/S. Dawson

Tawagar jami'ai daga Birtaniya a kungiyar da ke yaki da bazuwar makamai masu guba ta duniya (OPCW) ta fitar da wani bayani a shafin Twitter cewa an hana mata shiga yankin Douma na Siriya domin gudanar da bincike a wajen da ake zargin mahukuntan na Siriya sun kaddamar da hari da makami mai guba. Rasha da Siriya sun hana ba da dama ga kowa ya shiga yankin na Douma abin da ke nuna cewa Rashar da Siriya sun yi baki guda kan batun a cewar tawagar ta Birtnaiya.

Sai dai a wani labarin kuma mataimakin ministan harkokin wajen Siriya Fasial al-Mokdad, ya ba da tabbaci na cewa jami'an gwamnati sun gana da kwararrun na kungiyar ta OPCW, wadanda suka shiga kasar ta Siriya kwanaki uku da suka gabata kamar yadda mahukuntan na Siriya suka bukaci shigar tasu.