1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: An haramta hako ma'adanai

Abdul-raheem Hassan
July 4, 2019

'Yan sanda da sojoji a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun tarwatsa zanga-zangar masu hako ma'adinai bayan dakatar da kamfanin Glencore daga aikin hako ma'adanan ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3LauW
Konfliktfreie Kalimbi-Mine Kongo Minenarbeiter
Hoto: DW/J. van Loon

Dakatar da ayyukan kamfanonin hako ma'adanan na zuwa ne mako guda bayan mutuwar mutane 43 sakamakon zabtarewar kasa a wani kamfanin hako ma'adanin Jan Karfe wato Copper, wannan ya sa gwamnati daukar matakan dakatar da kamfanonin da ke aikin hako ma'adanan ta haramtacciyar hanya.

Sai dai kamfanonin na fargabar cin zarafi daga jami'an tsaro da suka yi killace harabar wuraren aiki. Jami'an tsaron kasar sun ki cewa komai kan matakin.