An hallaka wani minista a Libiya | Labarai | DW | 12.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka wani minista a Libiya

'Yan bindiga sun kashe Hassan al-Droui mataimakin ministan masana'antun ƙasar Libiya

'Yan bindiga sun bindige har lahira Hassan al-Droui mataimakin ministan kula da masana'antu na ƙasar Libiya. Wani jami'in gwamnati ya ce cikin daren jiya aka harbi shi a garin Syrte mai tashar jiragen ruwa, lokacin da ya kai ziyara zuwa mahaifarsa. Marigayi Hassan al-Droui ya kasance ɗaya daga cikin tsaffin wakilai gwamnatin wucin gadi, lokacin juyin-juya hali na ƙasar.

Wannan ke zama hallaka wani babban jami'in gwamnati na farko, bayan kawar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi cikin shekara ta 2011. Tun lokacin ƙasar ta Libiya ta faɗa cikin ruɗanin siyasa da tattalin arziki da zamantakewa, da rashin wata tsayayyiyar gwamnati da ta ke da cikekken iko da ƙasar baki ɗaya, inda tsageru 'yan bindiga ke ci gaba da tafiyar da lamura.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane