An hallaka wani jigon ′yan adawa a kasar Burundi | Labarai | DW | 08.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka wani jigon 'yan adawa a kasar Burundi

Matsalolin siyasa a kasar Burundi suna kara dagulewa sakamakaon kai hare-hare kan masu adawa da gwamnatin kasar.

Rahotanni daga Bujumbura babban birnin kasar Burundi na nuna cewar 'yan bindiga dadi sun hallaka mai magana da yawun daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa na kasar.

Marigayi Patrice Gahungu ya gamu da ajalinsa lokacin 'yan bindiga suka bude masa wuta kusa da gidansa da ke birnin Bujumbura a daren jiya Litinin, kamar yadda jam'iyyar UPD ta tabbatar, kuma ya kasance daya daga cikin masu adawa da Shugaba Pierre Nkurunziza.

Shugaba Nkurunziza ya na fuskantar matsin lamba bayan tazarce a wa'adi na uku, abin da ya jefa kasar ta Burundi cikin yanayi na rashin tabbas a siyasance da kuma kashe-kashen masu magoya bayan gwamnati da adawa da ita.