An hallaka sojoji a hare-hare a Masar | Labarai | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka sojoji a hare-hare a Masar

Kimanin mutane 26 ne aka bada labarin rasuwarsu sanadiyyar harin roka da na bam da aka kai a arewacin yankin Sinai na kasar Masar a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mafi yawan wanda suka rasu din sojoji ne da ke fafutuka wajen yaki da masu tsaurin kishin addini da ke tada kayar baya a yankin.

An dai kai harin na roka ne a hedikwatar rundunar 'yan sandan kasar da ke Al-Arish gami da wani sansanin soji da rukunin gidajensu, yayin da aka tada bam a wata mota a kofar shiga sansanin sojin.

Kungiyar nan ta IS reshen Masar ta ce ita ce ta kai harin kuma ta yi shi ne a matsayin ramuwar gayya kan irin yadda mahukuntan Masar din ke cin zarafin magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi, wanda wasunsu ke tsare yayin da aka yankewa wasu hukuncin kisa.