An hallaka masu aikin rigakafin chutar shan inna a Najeriya | Labarai | DW | 08.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka masu aikin rigakafin chutar shan inna a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun hallaka kimanin mutane tara masu aikin rigakafin chutar shan inna a garin Kano na Arewacin Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun hallaka kimanin mutane tara masu aikin rigakafin chutar shan inna, a garin Kano na arewacin Tarayyar Najeriya.

Mazauna garin da 'yan sanda sun ce lamarin ya faru cikin hare hare guda biyu, a wasu cibiyoyin kula da alluran rigakafin chutar ta shan-inna wadanda ke birnin. Daga bisani maharan sun tsere.

Najeriya tana cikin kasashe uku na duniya da suka rage dauke da chutar, sun hada da Afghanistan da Pakistan.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman