An hallaka jami′an tsaron Masar fiye da 50 | Labarai | DW | 21.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka jami'an tsaron Masar fiye da 50

Tsageru dauke da makamai sun hallaka jami'an 'yan sanda na kasar Masar fiye da 50 cikin wani hari kusa da birnin Alkahira fadar gwamnati.

Majiyoyin tsaro na kasar Masar sun tabbatar da cewa fiye da jami'an tsaro 50 aka hallaka lokacin da tsageru masu dauke da makamai suka harba makamin roka, wadanda suka hallaka sun hada da manyan jami'an 'yan sanda 20 da kuma sabbin dauka 34, sakamakon faruwar lamari a yankin kudu maso yammacin birnin Alkahira fadar gwamnatin kasar.

Hukumomi sun ce an fara musanyen wuta tun daga daren Jumma'ar da ta gabata, kuma harin ke zama mafi muni da tsageru suka kai kan hukumomi tsaron kasar ta Masar. Gwamnatin Shugaba Abdel Fattah al-Sisi ta mayar da hankali kan ganin an samu cikakken tsaro a kasar ta Masar wadda take samun hare-hare daga kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai, inda lamarin ya rincabe tun bayan kifar da gwamnati Shugaba Mohamed Mursi na kungiyar 'yan Uwa Musulmai a shekara ta 2013.