An halaka akalla mutane 13 a Zirin Gaza | Labarai | DW | 27.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An halaka akalla mutane 13 a Zirin Gaza

An katse tattaunawar da ake yi da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan Falasdinawa bayan wani fada a Zirin Gaza tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 13. Mutane da suka rasa rayukansu sakamakon harin bama bamai da harbe harbe su ne mafi yawa da aka taba samu a rana daya a rikicin cikin gida tsakanin Falasdinawa tun bayan da Hamas ta lashe zaben ´yan majalisar dokoki a bara. Yanzu haka dai masu shiga tsakani na kokarin ganin an sako akalla magoya bayan Hamas su 19 da wasu ´yan bindigan Fatah suka yi garkuwa da su a lokacin fadan. Tun wasu makonni da suka wuce sassan biyu dai na kokarain kafa wata gwamnatin hadin kan kasa to amma an dakatar da tattauwar sakamakon wannan rigima.