An haifi Adolf Hilter ne a ƙasar Austriya | Amsoshin takardunku | DW | 10.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

An haifi Adolf Hilter ne a ƙasar Austriya

Manyan ƙasashe masu ƙawance da Hitler a lokacin yaƙin dai sun haɗa da Japan da Italiya.

Adolf Hitler

Adolf Hitler

An haifi Adolf Hilter ne a ranar 20 ga watan afirilun shekara ta 1889 a ƙasar Austriya da ke nan Turai.

Adolf Hitler ya kafa wata jam'iya da ake kira National Socialist German Workers Party da ta rikiɗe zuwa Jam'iyar NAZI, wadda kuma ta bashi damar kasancewa shugaban Jamus ko Chancellor daga shekarar 1933 zuwa 1945.

Hitler ya yi yaƙin duniya na farko, kuma har ya taɓa zaman jarun a lokacin da aka zarge shi da neman kifar da gwamnati a yankin Bavariya da ke gabashin Jamus a 1923. Sai dai daga bisani Adolf Hitler ya samu goyon bayan al'umar Jamus na wancan lokaci, a lokacin da ya fara farfagandar adawa da tsarin jari hujja da mulkin kwaminisanci da kuma nuna tsana ga Yahudawa da kuma baƙaƙen fata ko kuma baƙi.

A shekarar 1939 Hitler ya ƙaddamar da yaƙi akan ƙasar Poland da nufin mamaye ta da kuma yaɗa manufofinsa na ‘Yan NAZI da ke ɗora Jamusawa akan kowane jinsi. Wannan mamaya da Hitler ya yi akan Poland ta sanya Ingila da Faransa ƙaddamar da yaƙi akan Jamus- lamarin da kuma ya kai ga fara yaƙin duniya na biyu.

A shekaru uku da fara wannan yaƙi sojojin NAZI na Hitler sun kama ƙasashe da dama da ke Turai da Afirka da kuma wasu ƙasashe da ke kudancin Asiya. Manyan ƙasashe masu ƙawance da Hitler a lokacin yaƙin dai sun haɗa da Japan da Italiya. To sai dai kuma mamayar da Sojojin Hitler suka yi wa wasu yankunan ƙasar Rasha ta sanya Sojojin ƙawance samun galaba akan na Jamus da ƙawayenta.

A duk tsawon shekarun da aka shafe ana wannan yaƙi dai, aƙalla fararen hula miliyan 17 ne suka rasu bayan Yahudawa miliyan shida da aka yi wa kisan ƙare dangi da aka fi sani da sunan Holocaust.

Ana gaf da kawo ƙarshen yaƙin duniyan na biyu da kuma kama birnin Berlin, Adolf Hilter ya auri wata farkarsa mai suna Eva Braun, kuma domin kauce wa shiga hannun Sojojin Soviet, Hitler da matarsa sun kashe kansu har lahira a ranar 30 ga watan Afirilun 1945.

Wasu bayanai na cewar an ƙona gawar Hitler da matarsa ne kafin isar Sojojin Soviet maɓuyarsa a Berlin, wasu kuma na cewar lugudan wuta daga Sojojin na Soviet ne ya yi kaca-kaca da gawar tasu.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas