1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gwabza sabon faɗa a gabacin Ukraine

May 15, 2014

An yi wannan gumurzu ne bayan da a ranar Laraba ɓangarorin da ke ƙoƙarin yin sulhu a rikicin na Ukraine suka kasa cimma wani sakamako a taron da suka yi a birnin Kiev.

https://p.dw.com/p/1C0hn
Ostukraine Krise Slowjansk 15.05.2014
Hoto: Reuters

Duk da ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya da ake yi baya bayan nan, dakarun gwamnatin Ukraine da 'yan awaren gabacin ƙasar sun sake gwabza faɗa. Kafofin yada labaru sun ce an yi musayar wutar ne a garuruwan Slavyansk da Kramatorsk da ke zama cibiyar masu fafatuka da ke goyon bayan Rasha. 'Yan awaren sun ba wa gwamnatin riƙon kwaryar birnin Kiev wa'adin sa'o'i 24 ta janye dakarunta, ko kuma su kai musu hari na a yi ta ta kare. A ranar Laraba dai a birnin Kiev aka gudanar da taron sasanta rikicin ƙasar ba tare da cimma wani sakamako na a zo a gani ba. Sai dai mahalarta taron sun ce sun amince da su ci gaba da tattaunawa a ranar Asabar mai zuwa. Halin da ake ciki a Ukraine kuma zai kasance batun da wani taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Amirka, Birtaniya, Faransa da kuma Jamus, a birnin London, zai mayar da hankali kai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane