An gwabza faɗa tsakanin sojojin Mali da na MNLA | Labarai | DW | 08.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gwabza faɗa tsakanin sojojin Mali da na MNLA

An ba da rahoton cewar an yi musanyar wuta ta bindigogi tsakanin sojojin Mali da dakarun ƙungiyar 'yan tawaye na MNLA a kusa da garin Menaka da ke a yankin arewaci na ƙasar.

Wasu majiyoyin soji sun ce an kashe dakarun ƙungiyar 'yan tawaye na Abzinawa su guda uku kana aka cafke wasu, yayin da ɗaya sojin gwamnati ya jikkata. Faɗan ya faru ne a sailin da wasu mutane ɗauke da makamai a yankin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar suka yi wa sojojin gwamnatin Mali kwanton ɓauna waɗanda ke yin sintiri.

Kuma faɗan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya kammala wata ziyarar aiki a ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh