An gurfanar da wasu ƙarin ′yan adawa a Masar | Labarai | DW | 25.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gurfanar da wasu ƙarin 'yan adawa a Masar

Daga cikin waɗanda aka gurfanar har'da Mohammed Badie jagoran Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi.

A Masar an gurfanar da jagoran Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi Mohammed Badie tare da wasu jama'ar kusan 700 magoya bayan hamɓararran shugaban ƙasar wato Mohammed Morsi a gaban wata kotun.

Bisa zargin da ake yi musu na tinzira jama'a ga aikta kisan wasu 'yan adawar a tashin hankali da aka yi a birnin Alƙahira a gaban cibiyar ƙungiyar a cikin watan Augutan da ya gabata. Hakan kuwa na zuwa ne kwana ɗaya bayan da wata kotun a kudancin ƙasar a garin Minya ta yanke hukumcin kisa a kan wasu magoya bayan Ƙungiyar na 'Yan Uwa Musulmi su 259 saboda samunsu da laifin tinzira jama'a. Abin da ya janyo tsokaci na ƙasashen duniya da kuma martanin na ƙungiyoyin kare hakin bil adama.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe