An gudanar da zaben shugaban kasa a Benin | Siyasa | DW | 06.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An gudanar da zaben shugaban kasa a Benin

'Yan takara 33 ne suka fafata da juna a zaben shugaban kasar Benin na ranar Lahadi. Benin dai ita ce kasa ta farko a Afirka mai amfani da harshen Faransanci da ta rungumi tsarin demokaradiyya.

Benin Wahlen Sébastien Ajavon

Babban hoton dan takara Sébastien Ajavon

Rahotanni daga jamhuriyar Benin na cewa al'ummar kasar ta kada kuri'ar zaben shugaban kasa a cikin konciyar hankali da lumana. Tuni ma dai aka rufe runfunan zabe a karfe hudu na yammacin wannan Lahadi har ma aka fara kidayar kuri'un.

A halin yanzu dai 'yan takara guda biyar ne daga cikin 33 da ke neman kujerer shugabancin kasar ta Benin ake ganin za su taka wata rawar gani dangane da wannan zabe zagaye na farko na ranar Lahadi, cikin su kuwa akwai Lionel Zinsou masanin tattalin arziki wanda shugaban kasar mai barin gado Yayi Boni ya dorawa nauyin jagorancin gwamnatin kasar a watan Yuni na 2015, wanda da ke a matsayin dan takara na jam'iyya mai mulki ta FCBE.

Benin Wahlen Patrice Talon

Magoya bayan dan takara Patrice Talon

Akwai kuma Patrice Talon dan shekaru 57 da haihuwa dan asalin birnin Ouidah wanda ya jagoranci fannin noman auduga, da tashar ruwan Cotonou da ke a matsayin fannoni biyu da tattalin arzikin kasar ta Benin ke tinkaho da su, Akwai kuma Sebastien Ajavon wani hamshakin dan kasuwa dan shekaru 51 da haihuwa, kuma ana ganin kusancin sa da dan majalisar nan Rachidi Gbadamassi zai kawo masa kuri'u masu yawa a yankin arewacin kasar. Sannan akwai Abdoulaye Bio Tchané da Pascal Irénée Koupaki.

Benin Wahlen Pascal Irénée Koupaki

Dantakara Pascal Irénée Koupaki

Da farko dai an tsaida ranar 28 ce ga watan Febrairu da ya gabata a matsayin ranar gudanar da zaben, amma kuma aka dage shi ya zuwa ranar shida ga watan Maris sakamakon latti da aka fuskanta wajan bugawa da kuma rabon katocin masu zaben da yawan su ya kai mutun miliyan hudu da dubu dari bakoye a wannan karamar kasa ta Yammacin Afirka.

Sauti da bidiyo akan labarin