An gudanar da bikin Maulidi a cikin ƙasashe musulmi | Zamantakewa | DW | 15.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An gudanar da bikin Maulidi a cikin ƙasashe musulmi

Musulmai da Kiristoci sun yi taron Maulidi, domin tabbatar da haɗin kai tsakanin mabiya addinan a Najeriya

A dai-dai lokacin da Duniya baki ɗaya ke Bukukuwan Tunawa da ranar haihuwar Annabi Mohammadu (SAW) manyan limaman Coci-coci a Tarrayar Najeriya suma sun fara halarltan bukukuwa da tarurrakan taya Musulman duniya murnan wannan rana. Domin ƙara kulla danƙwan zumunci da fahimtar juna, da ɗorewar zaman lafiya, don magance tashe-tashen hankula.To sai dai shagulgulan bikin wannan shekara sun sha banban da na sauran Shekarun da suka gabata, domin kuwa a wannan karon manyan Limaman Coci -coci sun kasance wasu daga cikin masu halaltan taron Maulidin Nabiyi da ake yi a ko'ina domin kara ƙarfafa kyakkyawar dangartaka ta fahimtar juna tsakanin Musulmai da Kiristoci, a wani mataki na warware wasu daga cikin matsaloli da ke addabar Musulmi da Kirista.

Alaramman Abdulrahman Mohammed Barnawa wani babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya da ke zaune a garin Barnawa, wani yanki na ɓangaren kudancin Kaduna, wanda tun da farko ya yi nuni da cewar fa'idar Maulidi ita ce faɗakar da duk wani Musulmin duniya irin rayuwar Annabi Mohammad, da kuma irin kyakkywar dangartakar da sauran al'umma domin su rika yin koyi da shi. Sannan nan kuma a kan tunatar da abokanan zama da suma ba Musulmai ba, yadda za a zauna lami lafiya domin samun damar dorewar zamantakewa tsakanin Musulmai da Kiristoci, ya ce "Ba mu taba samun Kiristoci ba sun shigo cikin wannan Maulidi sai dai na wannan karon, a saboda haka muna yin godiya ga maɗaukaki sarki Allah da damar da ya ba mu domin samun hada kai, don ci-gaban al'umman wannan ƙasa."

Pastor Yohanna Buru shi ne babban limamin Coci Christ Evengelical Intercessary Fellowship a Najeriya, da ya halalci taron Maulidin da tawagar pastocinsa domin taya Musulmai murnan wanan rana. Ya ce: Zuwa wajen wannan taron Maulidi abu ne da ya zamo masa wajibi, saboda a ranar tunawa da haihuwar Annabi Isah amincin Allah da tsira su tabbata a kansa, ɗaruruwan Musulmai ne suka je gidansa, domin taya shi murna, a sabili da haka, wannan gayyata da aka yi masa, abu ne da ya ji daɗi sosai, wannan ne ya sanya shi zuwa wannan wuri da sauran masu wa'azi, a sauran wuraren bauta wa Allah a Coci-coci domin ƙara ƙulla ƙawance da kuma ƙarfafa kyakkyawar dangartaka tsakanin Musulmai da Kiristaco tare da marasa addinai, domin kawo zaman lafiya a cikin ƙasa.

Malam Mohamed Gambo Abdullari ya kasance ɗaya daga cikin malaman da suka shirya wannan Maulidi a garin Kaduna da suka gayyato Kiristoci da ke ƙara bayar da haske kan dalilin gayyato makwabtan su limaman Coci-coci domin yin wannan biki tare. Inda Ya bayyana cewa suna san ganin malamai sun haɗa kai, domin kawo ƙarshen zubar da jinin bayin Allah da kai wa wuraren ibadu hare-hare, ba dare da raba.Pastor Maxuel Sanda ya kasance ɗaya daga cikin malaman addinin Kirista da suke nuna farincikin su game da halaltan wannan Maulidi. Ya ce "Na ji dadin zuwa wannan wuri, kuma ina mai taya Musulmai murna da zagawowar wannan rana." To sai dai har kullun Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira bisa Musulmi da Kirista kan fahimtar juna da kuma daina tayar da hankalin juna.Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saka wannan rana ta zamo ranar hutu ga ɗaukacin al'umman Musulmin Najeriya domin gudanar da Bukukuwar maulidi da ziyarce-ziyarce 'yan uwa da abokan arziki.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Suleiman Babayo