An gona gawar matashiyar Indiya da ta mutu sanadiyar fyade | Labarai | DW | 30.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gona gawar matashiyar Indiya da ta mutu sanadiyar fyade

An kona gawar daliba mai koyon aikin likita na Inidya, wadda ta mutu sakamakon raunukan da ta samu

An kona gawar daliba mai koyon aikin likita na Inidya, wadda ta mutu sakamakon raunukan da ta samu, yayin da wasu gungun mutane su ka yi mata fyade, a Delhi babban birnin kasar cikin wannan wata na Disamba.

Hukumomin sun kama mutane shida, wadanda yanzu su ke fuskan hukuncin kisa, saboda zargin aikita wannan laifi.

Bayanai sun ce dalibar 'yar shekaru 23 da haihuwa mai koyon aikin likita, tana shirin aure cikin watan Febrairu mai zuwa, kuma tare su ke tafiya da wanda zai aureta lokacin da lamarin ya faru, inda maharan su ka lakkada musu duka, bayan sun yiwa matashiyar fyade. Kuma haka ya janyo zanga zanga cikin kasar baki daya.

Firaministan kasar ta Indiya Manmohan Singh da shugabar jam'iyyar Congress mai mulki Sonia Gandhi na cikin wadanda su ka tarbi gawar a filin saukan jiragen saman Delhi, bayan daukawa da jirgin na musamman daga Singapore, inda dalibar ta cika a wani asibiti.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh