An gaza cin kyautar Mo Ibrahim | Labarai | DW | 14.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza cin kyautar Mo Ibrahim

Hukumar da ke ba da kyautar Mo Ibrahim ta shekara ta sanar da cewar a wannan shekara ma babu wanda ya ci kyautar.

Hukumar wacce aka kafa a shekarun 2006 na ba da kyautar ga tsofin shugabannin da gwamnatocin Afirka, wanda suka taka rawar ganin wajen samin ci gaba da kuma ɗorewar demokraɗiyya a cikin ƙasahensu.

Da yake magana shugaban kwamitin Ahmed Salim Ahmed tsohon sakataran ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka a lokacin OUA, kana tsohon shugaban gwamnatin Tanzaniya. Ya ce bayan dogon nazarin kwamitin bai ga wanda ya cancanci samin kyautar ba, ta dala miliyan biyar. Daman dai a kwanan baya, Mo Ibrahim ɗin wani attajirin ɗan kasuwa na ƙasar Sudan wanda ake yin kyautar da sunansa,ya yi kakausar suka ga salon mulki na shugabannin Afirka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal