An gaza cimma yarjejeniya a rikicin Sudan ta kudu | Labarai | DW | 06.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza cimma yarjejeniya a rikicin Sudan ta kudu

Masu shiga tsakani a rikicin kasar Sudan ta Kudu, sun ce bangarorin da ke gaba da juna na shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun gaza cimma yarjejeniya

Masu shiga tsakani a rikicin kasar Sudan ta Kudu, sun ce bangarorin da ke gaba da juna na shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun gaza cimma yarjejeniya, lamarin da a cewar mahukuntazkia iya janyo kakaba takunkumi.

Faraiministan kasar Ethiopia, ya ce tattaunawar da aka yi da tsakar daren jiya dama wadda aka yi yau Juma'a ba su samar da sakamako ba.

Takaddama tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Machar dai ya haddasa mutuwar dubun dubatan kabilun kasar da muzgunawa mai tsanani ga kabilun kasar da dama, lamarin da a yanzu ke kokarin tilasta kasar shiga cikin karin matsaloli, musamman na karancin abinci.

A wannan makon dai Majalisar Dinkin Duniya, ta yi barazanar kakaba takunkumi kan duk wani da ya kawo tsaiko ga kokarin da ake yi na kawo sasantawa a rikicin na Sudan ta Kudu.