An gaza cimma matsaya tsakanin Iran da ƙasashen duniya | Labarai | DW | 25.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza cimma matsaya tsakanin Iran da ƙasashen duniya

An tsawaita tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da ƙasashen duniyar har zuwa shekarar baɗi domin cimma wata yarjejeniya ta dakatar da shirin nukiliyar na Iran.

Iran da sauran mayan ƙasashen duniya guda shidda sun watse baram-baram ba tare da cimma wata yarjejeniya ba a taron, da ministocin harkokin waje na ƙasashen suka gudanar a Vienna da nufin samun daidaituwa a kan shirin nukiliya na Iran ɗin.

Ministocin ƙasashen na China da Ingila da Faransa da Rasha da Amirka da kuma Jamus,sun ce an ɗan samu ci gaba a tattaunawar. Sai dai sun ce kuma ya zama dole a tsawaita wa'adin tattaunawar wanda ya kau a jiya har ya zuwa baɗi domin cimma matsa ɗaya ta ƙarshe.