An gaza cimma matsaya guda a tsakanin Jam`ìyyun ANPP da AC a Nigeria | Labarai | DW | 09.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza cimma matsaya guda a tsakanin Jam`ìyyun ANPP da AC a Nigeria

Jam´iyyun ANPP da AC a Nigeria sun dage taron da suka shirya yi a yau din nan, don duba yadda kawancen da suka shiga da juna zai kasance.

An dai dage taron na yau ne sakamakon yadda yan takarar guda biyu, wato Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar, suka gaza cimma yarjejeniyar barwa guda daga cikin su.

A yanzu haka dai a cewar rahotanni yan takarar biyu na ci gaba da tuntubar juna, don cimma matsaya guda a game da wanda za´a marawa baya don fafatawar a zaben shugaban kasar mai zuwa.

A dai watan disambar bara ne jamiyyyun guda biyu suka rattaba yarjejeniyar kulla kawance, don tunkarar jamiyyar PDP mai mulki a zabubbukan da za´a gudanar na matakai daban daban, a watan afrilun wannan shekara.

Ya zuwa yanzu dai harkokin siyasa a kasar tuni suka fara daukar zafi, sakamakon yadda lokutan zabe ke kara karatowa.

Hukumar zabe ta kasar mai zaman kanta dai ta INEC, tace a ranakun 14 da 21 ne na watan Afrilun wannan shekara ,aka ware don gudanar da sabbin zabubbukan na matakai daban daban