1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya zata fuskanci kalubalan yanayi

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
November 15, 2021

An bayyana taron sauyi ko kuma dumamar yanayi na Majalaisar Dinkin Duniya da aka kammala a Glasgow da cewa ya gaza, bayan da kasashen Indiya da Chaina da ke zaman wadanda suka fi gurbata muhalli suka ki ba da hadin kai.

https://p.dw.com/p/431KJ
Essen | Schornstein des Müllheizkraftwerk Essen-Karnap
Hoto: Jochen Tack/picture alliance

Taron dai ya so cimma matsaya kan gaggauta rage da fitar da hayakin kwal da albarkatun man fetur masu gurbata muhalli da ke da nasaba da dumama ko kuma sauyin yanayi, sai dai hakan taron na COP26 bai cimma ruwa ba. Ko da yake mahalarta taron sun amince da kara daukar matakan yaki da dumama ko sauyin yanayin tare kuma da tallafa wa kasashe masu tasowa, sai dai a inda gizon ke saka shi ne wajen bayar da tallafin. Mahalartar taron sun yanke shawarar gabatar da sababbin kudirori a taron shekara mai zuwa, abin da zai ba su damar cimma muradun ci-gaba mai dorewa a fannin dumamar yanayi na rage dumin da duniya ke fuskanta na da shekara ta 2030. A jawabinsa ga manema labarai bayan kammala taron na sauyi ko dumamar yanayi na bana, firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana taron na COP26 a matsayin wanda aka cimma yarjejeniyar kawo gyara, duka da sauyin da aka samu a daidai lokacin da ake kammala shi yana mai cewa: "Duk da farin cikin da nake ciki a wannan lokacin, na kuma samu kaina cikin rashin jin dadi. Ga wasu kasashen, tuni sauyin yanayi ya zame musu zabi tsakanin rayuwa da mutuwa. Kasashen da tsaunukansu ke karewa, gonakinsu ke zama hamada kana gidajensu ke rushewa saboda mahaukaciyar guguwa na cike da fatan ganin an samar musu da mafita. Da yawanmu muna da wannan fatan, kuma muna son kai wa ya zuwa ganin karshen matsalar. Sai dai ba kowa ke da wannan niyya ba, ba kuma za mu iya tilasta kasar da ke da cikakken 'yanci su dauki irin matsayarmu ba, sai dai mu roke su ha mu cimma matsaya guda, Wanna shi ne diplomasiyyar, ra'ayinsu ne kuma shi suka zaba za su yi."

Masu fafutikar kare muhali sun bayyana taikaicinsu

UN-Klimakonferenz COP26 in Glasgow | Proteste
Hoto: Dominika Zarzycka/NurPhoto/picture alliance

Kasashe da dama da suka hadar da kananan tsaunuka, sun bayyana rashain jin dadinsu kan matakin da Indiya ta dauka a karshen taron, inda ta ce sai dai ta rage gurbatacciyar iskar da take fitarwa sakamakon makamashin kwal maimakon dakatarwa baki daya. Makamashin na akwal dai na zaman babban abin da ke janyo fitar gurbatacciyar iska da ke gurbata yanay, hakan kuma na zaman babban musabbabin sauyi ko kuma dumamar yanayi. Masu fafutuka da dama kamar Jack Steve Ootieno da ke fafutukar kare muhalli a kasar Kenya, sun nuna damauwarsu kan yadda taron na COP26 ya gudana. Ma shekaru 25 a duniya, Ootieno ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa COP26 ya gaza:  Ya ce: "In har za su yi ta kiraye-kirayen da ba za su iya ganin sun tabbata ba, a ganin taron COP26 ya gaza. Gazawa ce ga duniya ba ki daya. Dumamar yanayi na karuwa, ambaliyar ruwa da fari. Kamfar ruwa na sanya koguna kafewa, abin da zai janyo koma baya ga noman kifi. Matsalar yunwa za ta karu a duniya baki daya." 

Duniya ta gaza wajen shawo kan dummar yanayi

Shugaban taron  COP26  Alok Sharma
Shugaban taron COP26 Alok SharmaHoto: Phil Noble/REUTERS

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, shugaban taron na COP26 a bana Alok Sharma ya nunar da cewa yarjejeniyar da ake son cimma na cikin garari, domin kuwa duniya na daf da shiga hadari kan dumamar yanayin. Kasashen Chaina da Indiya dai na zaman manyan kasashe da ke fitar da gurbatacciyar iska ta makamashin kwal, sai dai ana daf da kammala taron suka sauya ra'ayinsu daga dakatar da fitar da iskar zuwa rage fitar da ita. A nasu bangaren, kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya sun amince da bin wani tsari, inda daga shekara ta 2023 za su rinka samar da dalar Amirka biliyan 100 duk shekara ga kasashe masu tasowa kan gurbatacciyar iskar da suke fitarwa domin dakile dumamar yanayin duk da cewa sun yi irin wannan alkawarin a baya ba tare da sun cika shi ba.