An gargadi Sudan data amince da aika dakaru Darfur kafin karshen shekara | Labarai | DW | 21.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargadi Sudan data amince da aika dakaru Darfur kafin karshen shekara

Wani babban jamiin Amurka ya gargadi gwamnatin Sudan cewa dole ne ta amince da aikeawa da dakarun MDD zuwa Darfur nan da karshehn shekara ko kuma ta fuskanci fushin kasa da kasa.

Jakadan Amurka na musamman zuwa Sudan Andrew Natsios yace ya sanarada shugabannin Sudan cewa dole ne su bar tawagar MDD mai mutum 60 da yanzu haka suka makale a Khartoum da su shiga yankin darfur.

Ya kuma bukaci gwamnati data amince a rubuce,game shirin komitin sulhu na aikewa da dakaru 20,000 zuwa Darfaur domin kawo karshen tashe tashehn hankula da sukayi sanadiyar rayukan mutane fiye da 200,000 wasu kuma miliyan 2.5 tilas suka tsere daga gidajensu.