An gargadi sabuwar gwamnatin Girka | Labarai | DW | 27.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargadi sabuwar gwamnatin Girka

Sabuwar gwamnatin Girka tana shirin bayyana matakan bunkasan tattalin arziki

Sabuwar gwamnatin kasar Girka karkashin firaminista Alexis Tsipras na jam'iyyar Syriza tana shirin bayyana matakan da za a dauka domin tunkarar tattalin arzikin kasar da ke cikin rudani yayin da ake bin kasar dinbin bashi. Jam'iyyar ta Syriza ta samu nasara sabo yadda ta nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihu da ake aiwatarwa a kasar.

Kasashen Turai sun gargadi sabuwar gwamnatin kasar ta Girka kan cewa babu wata dama na yabe mata wani bashin kirki daga cikin kudaden da ake bin kasar. Sabon firaminista Tsipras ya yi rantsuwar kama aiki bayan shiga yarjejeniya da wata karamar jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi.