An gano wasu gawaki biyar a Mali | Labarai | DW | 24.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wasu gawaki biyar a Mali

Hukumomin a kasar sun gano gawaki biyar na sojoji, kusa da barakin Soja na Kati. inda ake kyautata zaton cewa lamarin ya faru ne tun juyin mulkin shekara ta 2012

Gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita na kasar ta Mali, ta sha alwashin samun haske kan bacewar da wasu sojojin Laima na kasar suka yi, lokaci kalilan bayan juyin mulkin da Janar Amadou Sanogo, wanda ke da mukamin Kaftan a wacan lokaci ya jagoranta, wanda shima a halin yanzu yake tsare sakamakon kamashi da laifin batar da wasu mutanen.

Da yake magana kan wannan batu wani kusa a ofishin ministan shari'a na kasar ta Mali, ya ce gawakin an gano su ne a daran Lahadi wayewar wannan Litinin din, hannayan su a daddaure, sannan kuma an daure fiskokinsu.

A halin yanzu dai adadin gawakin da aka gano ya kai talatin, wadanda dukanninsu an tono su ne kusa da barakin Kati, da ke a nisan kilo mita kimanin ashirin daga birnin Bamako.

Hukumomin kasar ta Mali dai, sun sanar da cewa Janar Yamoussa Camara, ministan tsaron kasar a tsofuwar gwamnatin ta mulkin soja, an kama shi ne tare da wasu jagororin juyin mulkin guda uku a makon da ya gabata, bisa dalilai na bincike.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Usman Shehu Usman