An gano wani shirin al-Shabaab na kai sabbin hare-hare a Somaliya | Labarai | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wani shirin al-Shabaab na kai sabbin hare-hare a Somaliya

'Yan takife a Somaliya sun shirya kai hare-hare a matsayin sojin gona na rundunar zaman lafiyar AU a kasar.

Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka AU a Somaliya sun ce sun samu bayanan cewa sojojin sa kai masu alaka da kungiyar al-Kaida sun shirya kai hare-hare a Somaliya a cikin unifom na sojojin AU. Jami'ai suka ce mayakan kungiyar al-Shabaab sun sace rigunan sojoji daga wasu sansanonin rundunar AMISOM kuma 'yan tarzoman sun shirya yin sojin gona don kai hare-hare. A ranar 15 ga watan Janeru sojojin Kenya da dama da ke aiki karkashin lemar rundunar AMISOM sun salwanta a wani hari da al-Shabaab ta kai kan sansaninsu da ke garin El Adde na kudancin Somaliya. 'Yan tarzoman sun ce sun kashe sojoji fiye da 100 a harin kan sansanin da ke kusa da iyakar Somaliya da Kenya, amma har yanzu gwamnatin birnin Nairobi ba ta fid da alkaluman yawan sojonjinta da aka halaka ba.