1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano takardun sirri a gidan Biden

Binta Aliyu Zurmi
January 12, 2023

A wani bincike da aka kaddamar a gidan Shugaba Joe Biden da ke Delaware an gano wasu takardun sirri da suka shafi gwamnati Amirka tun lokacin da yake mataimakin tsohon shugaba kasar Barrack Obama.

https://p.dw.com/p/4M6HP
USA, Washington | Joe Biden
Hoto: Kevin Dietsch/Getty Images

A ganawar da ya yi da namema labarai Shugaba Biden ya tabbatar da wannan lamari kuma ya ce yana bada hadinkan da ya kamata da bangaren shari'a a binciken da suke yi.

Tun a farkon watan Nuwamban bara ne aka fara bankado wadannan takardun a gidan shugaban, sai dai ba a fidda zancen ba sai a wannan Litinin din. Hakan na zuwa ne bayan sake samun wasu takardun a ofishin tsohon mataimakinsa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun wasu muhimman takardu a gidan babban jami'in gwamnati ba, a baya ma an sami wasu a gidan tsohon shugaban kasar Donald Trump.