1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano sabbin manyan kaburbura a Namibia

Mohammad Nasiru AwalNovember 25, 2005

Kungiyar kare hakkin dan Adam a kasar ta yi kira da a kafa hukumar gaskiya da sasantawa.

https://p.dw.com/p/BvUF
Shugaban Namibia Hifikepunye Pohamba
Shugaban Namibia Hifikepunye PohambaHoto: AP

Kasussuwa wasu ma kwarangwal din ne gaba daya a cikin unifom na tsofaffin mayakan kwatar ´yanci aka gano a cikin manyan ramuka guda 5 a lokacin wani aikin shimfida bututu a arewacin kasar Namibia a kusa da iyakarta da Angola. An dai binne mayakan kungiyar kwatar ´yancin ta PLAN ne lokacin yakin kwanaki 9 a kasar ta Namibia a cikin watan afrilun shekarar 1989. To sai dai daraktan hukumar kare hakkin bil Adam ta Namibia Phil Yah Nangoloh ya ce wannan ba sabon abu ba ne. Domin MDD ta na nan a wancan lokacin dab da ba wa kasar ´yanci kuma ya tabbata a fili cewa ATK zata janye daga kasar ta Namibia. To amma kwasan sai wani sabonrikici ya barke a yankin Ovamboland dake arewacin kasar. A wancan lokacin gawawwakin dai na yashe ne a cikin daji, a saboda haka MDD ta umarci ATK da ta binne su kamar yadda doka ta tanada. Nangoloh ya ce gwamnatin SWAPO da MDD dukkan su na da masaniya game da aukuwar wannan lamari.

“A gani na gwamnati na amfani da wannan abin ne don farfaganda, musamman saboda barakar dake tsakanin jam´iyar SWAPO dake mulki. Inda bangaren tsohon shugaba Sam Nujoma ke zargin bangaren tsohon ministan harkokin waje Hidipo Hamutenya da hada baki da ATK don aikata wannan ta´asa.”

Nangoloh ya ce akwai batutuwa da dama da ba´a fito fili aka fadi ba tun bayan samun ´yancin Namibia a cikin shekarar 1990. Ya ce har yanzu daukacin al´umar kasar ba su yafe wa juna ba. To amma duk da haka ana zamantare tsakanin farar fata wadanda a da suka goyi bayan mamayar da ATK ta yiwa kasar da bakar fata wadanda suka marawa kungiyar SWAPO baya. A saboda haka kungiyar kare hakkin bil Adam karkashin jagorancin Nangoloh ta yi kira da a kafa hukumar gaskiya da sasantawa nan take don gurfanad da duk wadanda suka aikata laifukan yaki da cin zarafin ´yan Adam a lokacin gwagwarmayar kwatowa Namibia ´yanci. Wannan hukumar zata taimaka a sasanta kuma share wannan mummunan tabo daga cikin tarihin kasar ta Namibia. Nangoloh ya ce dukkan bangarorin biyu wato ATK da kuma kungiyar SWAPO sun aikata wannan laifi. Amma yanzu gwamnati ba ta so a tabo wannan magana. So ta ke a ci-gaba da dorawa ATK kadai laifin aikata wannan ta´asa.

Watakila Namibia ka iya amfani da gano kaburburan a matsayin wata dama ta sasanta al´umar kasar shekaru 15 bayan samun ´yanci. To amma idan ba´a kafa wannan hukuma ba, ba za´a yafewa juna ba bare watakila ma a yi kokarin mantawa da abin da ya faru a zamanin baya, wato kenan za´a ci-gaba da zama ne ta ciki na ciki ba tare da an samu dawwamammen zaman lafiya ba.