1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano maɓoyar faransawan da Alqa´ida ta cafke a Arlit

September 27, 2010

Hukumomin Faransa sun ce a shirye su ke su tattana da Alqa´ida da zumar belin mutanen AREVA da ta yi garkuwa da su

https://p.dw.com/p/PNNr
Alqa´ida ta ɓoye faransawa AREVA a Sahara MaliHoto: Mohamed Mahmoud Aboumaaly

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya ce 'yan ƙasar biyar da a ka sace a yankin Arlit na jamhuriyar Nijar su na raye, kuma a na tsare da su ne cikin tsaunuka da ke arewacin ƙasar Mali. A yankin haƙar ma'adanai na jamhuriyar Nijar ɗin ne dai masu bindiga su ka kama Faransawa biyar ciki harda mace da mijinta da wasu biyu 'yan ƙasashen Togo da Madagaska, tun kwanaki sha ɗaya. Kakakin shugaban ƙasar ta Faransa ya ce su na tattaunawa da waɗanda ke tsare da mutanen, wato 'yan ƙungiyar Alƙa'ida na yammacin Afirka. Kakakin ya ce su na da hujjar cewa waɗanda a ka sacen na raye kuma a na tsare da su ne a cikin hamadar arewacin ƙasar Mali kusa da iyakar Aljeriya. Wani na kusa da fadar gwamnati a Paris da ya nemi a sakaya sunansa, kuma ya ke cikin masu tattauna yadda za'a sako mutanen, ya ce ya ga waɗanda a ka sacen da idanunsa, kuma su na nan ƙalau, kana sun faɗi hakan ne domin su tabbatarwa iyalan waɗanda aka sacen lafiyarsu lau.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi