An gano masu ɗauke da cutar Ebola a Laberiya | Labarai | DW | 31.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano masu ɗauke da cutar Ebola a Laberiya

Hukumar lafiya ta duniya WHO ko kuma OMS ,ta ce gwamnatin Laberia ta tabbatar da cewar mutane biyu sun kamu da ciwon zazzaɓi mai tsanani na Ebola.

Hukumar ta ce mutanen guda biyu waɗanda aka gano suna ɗauke da ƙwayoyin cutar, suna zaune ne a ga garin Foya da ke kan iyaka da Guinea da kuma Saliyio. Cutar wacce ta ɓulla a cikin farkon wannan wata a Guinea Conakry inda ta kashe mutane 70. Manazarta al'amuran kiwon lafiya na cewar tana da alamar bazuwa a cikin sauran ƙasashen yankin yammaci Afirka.

Tuni dai da Ƙasar Senegal ta rufe kan iyakarta da Guinea ,tare da haramta cin wasu kasuwannin ƙayukan ga jama'ar ƙasar da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar