1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwaki a birnin Bangui

March 29, 2013

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta gano gawarwaki kimanin 78 a titunan birnin Bangui na kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mako daya bayan kifar da gwamnatin Bozize.

https://p.dw.com/p/1871h
'Yan tawayen SelekaHoto: AFP/Getty Images

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Croix Rouge ko kuma Red Cross,ta bayyana cewar ta gano wasu gawarwakin da adadinsu ya kai 78 a titunan Bangui fadar gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka gano matattun mutane a kan titunan birnin tun bayan da 'yan tawaye suka kwace milki a makon jiya.
Yanzu haka dai gawarwakin na can zube a babban asibitin garin na Bangui domin baiwa danginsu damar zuwa ganinsu.
Kungiyar ta nuna damuwarta a dangane da halin da jama'a ke ciki a kasar inda ake fuskantar karancin maguguna da tsabtattun ruwa sha abun da kan iya kara tsananta yanayin da jama'an garin ke ciki.
Wani rahoto daga hukumar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta OCHA ya zargi 'yan tawayen Seleka da kisan fararen fulla tare da kwasar ganima a lokacin da suka auka wa babban birnin da nufin anshe iko daga shugaba Francois Bozize.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal