An gano bam ne ya tarwatsa jirgin saman Rasha | Labarai | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano bam ne ya tarwatsa jirgin saman Rasha

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya nunar da cewa kasar za ta hukunta wadanda ke da alhakin saka bam da ya tarwatsa jirgin saman fasinja mallakin kasar a sararin samaniyar Masar.

Gwamnatin Rasha ta tabbatar da cewa bam da aka dasa ya tarwatsa jirgin saman fasinja mallakin kasar lokacin da ya taso daga garin Sharm al-Sheikh na kasar Masar a kan hanyar zuwa Rasha dauke da mutane 224 wadanda suka hallaka baki daya. Masu bincike sun nunar da cewa an saka bam mai girma da ya kai kilo-gram daya a cikin jirgin saman.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi alkawarin hukunta wadanda suka aika laifin ko'ina suke cikin wannan duniya.

Rahotanni sun ce kasar ta Rasha ta kara kaimin hare-hare kan tsageru cikin kasar Siriya, tare da cewa za ta yi aiki da duk dokokin kasashen duniya wajen mayar da martani.