An gano bam a tsakiyar birnin Berlin na Jamus | Labarai | DW | 03.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano bam a tsakiyar birnin Berlin na Jamus

Bam ɗin mai nauyin kilo 100 an dasata ne tun lokacin yaƙin duniya na biyu, kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana.

Yan sanda a birnin Berlin na nan Jamus, sun ce wata bam da aka gano a kusa da babbar tashar jiragen ƙasa na birnin, ta hadasa tsaiko akan sha'anin zirga zirga na jiragen ƙasa da na ruwa.

Bam ɗin mai nauyin kilo 100 wacce aka dasa tun a lokacin yaƙin duniya na biyu, ƙwarraru sun ce ta ƙasar Rasha ce. yanzu haka dai an kwashe jama'ar da ke zaune a kusa da inda aka gano bam ɗin. Shekarun kusan satin bayan yaƙin duniya na biyu, har yanzu a kwai bama bama a ƙalla guda dubu uku da hukumomin Jamus ɗin suka yi amanar cewar suna a bizne a cikin ƙarƙashin ƙasa waɗanda basu tashi ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Awal Nasiru.