An gano asalin wadda ta kai harin kunar bakin wake a birnin Ankara | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano asalin wadda ta kai harin kunar bakin wake a birnin Ankara

Akalla mutane 37 suka rasu sannan fiye da 120 suka samu raunuka a harin kunar bakin waken birnin Ankara da ke zama irinsa na uku a birnin.

Hukumomi a kasar Turkiyya sun ce sun iya gano asalin wata mace da ke zama daya daga cikin wadanda suka kai mummunan harin kunar bakin wake a birnin Ankara a ranar Lahadi. Majiyoyin hukumomin tsaron kasar ta Turkiyya sun ce 'yar kunar bakin waken ta fito ne daga yankin gabashin kasar, kana kuma memba ce a haramtacciyar kungiyar Kurdawa ta PKK. Alkalumman da gwamnati ta bayar na cewa akalla mutane 37 suka rasu sannan fiye da 120 sun samu raunuka a harin kunar bakin waken da aka kai da mota a wata tashar motocin bas da ke kusa da dandalin Kizilly da ke birnin na Ankara. Wannan harin dai shi ne na uku da ya auku a tsakiyar birnin na Ankara a tsukin watanni biyar.