An gana tsakanin Bush da de Hoop Scheffer a Texas | Labarai | DW | 21.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Bush da de Hoop Scheffer a Texas

Shugaban Amirka GWB ya ce zai matsawa kawaye Amirka da su dauki karin nauyin tabbatar da tsaro a Afghanistan a daidai lokacin da ake kara samun asarar rayuka sakamakon sabbin hare hare na ´yan Taliban. Bush ya nunar da haka ne a ganawar da yayi da sakatare janar na kungiyar kawance ta NATO Jaap de Hoop Scheffer a gidan gonar shugaban da ke jihar Texas. Bush ya ce kafin NATO ta yi tasiri dole ne ta sauya ta zama wata kungiya da zata iya kalubalantar dukkan barazanar dake kasashe ke fuskanta. A na sa bangare mista de Hoop Scheffer ya ce har yanzu Afghanistan na zama wani bakin daga a yakin da ake yi da ´yan ta´adda.