1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fidda Alkama daga Ukraine zuwa Habasha

Ahmed Salisu
September 17, 2022

Wani jirgi da Majalisar Dinkin Duniya ta yi hayarsa don kai kayan abinci zuwa kasar Habasha ya bar kasar Ukraine dauke da tan dubu 30 na Alkama a wannan rana ta Asabar kamar yadda hukumomi a kasar ta Ukraine suka nunar.

https://p.dw.com/p/4H0cC
Ukraine | Krieg | Odessa | Getreideverschiffung
Hoto: Oleksander Gimanov/AFP/Getty Images

Shirin Abinci  na Majalisar Dinkin Duniya wanda shi ne ke yin wannan aikin ya ce za a hannanta Alkamar ce ga kasar ta Habasha da kuma Yemen wadanda ke kokarin shiga ja'ibar yunwa saboda gaza sayen Alkamar da kuma sauran kayan abinci dangin hatsi sanadiyyar yakin da Rasha ke yi a Ukraine.

Wannan jirgi shi ne irinsa na 3 da ya bar Ukraine din don sada abincin ga kasashen da ke bukata wanda hakan ya kawo yawan tan din Alkamar da aka fidda zuwa dubu casa'in.

A cikin watan Yulin da ya gabata ne dai aka bada damar fidda Alkamar daga Ukraine zuwa sauran sassan duniya bayan da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka shiga tsakani a wani zaman sulhu da aka yi tsakanin jami'an Rasha da Ukraine kan wannan batu.