An fatattaki masu zanga-zanga a Sudan | Labarai | DW | 30.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fatattaki masu zanga-zanga a Sudan

'Yan sandan Sudan sun amfani da hayaki mai sa kwalla kan tarin masu zanga-zanga da suka fito don zafafa matsin lamba ga gwamnatin mulkin soja da ta mika jan ragamar mulki a hannu farar hula.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a wasu unguwanni na  Bari, al-Mamoura da Arkaweit, da ke wajen birnin Khartum inda dubban masu zanga-zangar da suka fito suka yi dandazo. Wasu rahotanni daga gabashin kasar ta Sudan musamman a Gadaref, sun ce a can din ma 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar tare da tarwatsasu.
  
Jami'an tsaron kasar ta Sudan sun jibge askarawan rundunar RSF kan motoci da makamai a ko'ina cikin birnin a wani mataki na shirin ko ta kwana. Wannan al'amarin na zuwa ne duk da kiraye-kiranyen kwantar da tarzoma da kiyaye hakin masu zanga-zanga da hukumomin kare hakin dan Adam na kasa da kasa suka yiw a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan, duba da yadda aka samu kisan jama'a masu bore da adawa da gwamnatin mulkin soja a farkon wannan wata.